Nigerian news All categories All tags
Bayan murabus din sa jam'iyyar PDP ta maye gurbin Sanata Akpabio

Bayan murabus din sa jam'iyyar PDP ta maye gurbin Sanata Akpabio

Sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a majalisar dattawan Najeriya sun maye gurbin Sanata Akpabio da ya sauya shiga zuwa APC da Sanata Biodun Olujimi daga jihar Ekiti a matsayin shugaban marasa rinjaye.

Ita dai Sanata Biodun Olujimi ta tabayin mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti sannan kuma kafin samun sabon mukamin nata itace mataimakiyar mai tsawatarwa a zauren na majalisar dattawa.

Bayan murabus din sa jam'iyyar PDP ta maye gurbin Sanata Akpabio

Bayan murabus din sa jam'iyyar PDP ta maye gurbin Sanata Akpabio

KU KARANTA: Wata tsohuwa ta suma wajen kallon Atiku

Legit.ng dai ta samu cewa a farkon watan nan ne Sanata Godswill Akpabio dake zaman tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya sauya shekar sa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

A wani labarin kuma, A yayin cigaba da kokarin tunkarar zabukan gama-gari da za'a gudanar a shekarar 2019, jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress, APC ta fitar da tsarin jadawalin yadda zata gudanar da zabukan ta na fitar da gwani domin tunkarar zaben.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar jiya a garin Abuja dauke da sa hannun jami'in yada labaran ta mai rikon kwarya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel