An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

Kimanin jami'an tsaro na 'yan sanda guda talatin ne suka sadaukar da rayukan su wajen bautawa kasar su ta gado watau Najeriya cikin wata guda da ya gabata.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Akwa-Ibom, Adeyemi Ogunjemilusi, shine ya bayyana hakan yayin taron tsaro dangane da miyagun laifuka da aka gudanar cikin karamar hukumar Eket ta jihar a ranar Talatar da ta gabata.

An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, hukumar 'yan sanda reshen jihar tare da hadin gwiwar karamar hukumar ne suka dauki nauyin gudanar da wannan taro, inda babban jami'in ya ce Najeriya ta rasa 'yan sandan ta 30 cikin kwanaki talatin da suka gabata.

KARANTA KUMA: Cutar Gudawa ta Tsinkewa Mutane 400, ta kar 28 a Jihar Kano

Duk da cewar a kowace rana jami'an tsaro na sadaukar da rayukan su, sai dai abin takaici dangane da yadda ake ma su mummunan jifa tare da shafa ma su bakin fenti kamar yadda Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu akwai mutane 60 da suka shiga hannun hukumar da suka shahara da aikata miyagun laifuka musamman 'yan kungiyoyin asiri, inda za su fuskanci hukunci kamar yadda hukumar 'yan sandan ta tanadar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel