Harkar kwallo: Hukumar FIFA ta Duniya ta ja kunnen Najeriya

Harkar kwallo: Hukumar FIFA ta Duniya ta ja kunnen Najeriya

Mun samu labari cewa akwai yiwuwar a haramtawa Najeriya taka leda a Duniya a dalili d sabanin da ake samu a cikin kasar tsakanin Shugabannin Kungiyar kwallon kafa na Kasar watau NFF.

Harkar kwallo: Hukumar FIFA ta Duniya ta ja kunnen Najeriya

FIFA ta nemi a dawo da Amaju Pinnick kan kujerar sa

Ana rigima ne tsakanin Amaju Pinnick da Chris Giwa inda kowa yake ikirarin cewa shi ne Shugaban Hukumar NFF na kwallon kafar kasar. FIFA dai tace Amaju Pinnick ta sani a matsayin Shugaban harkar kwallo a Najeriya.

Yanzu haka Hukumar FIFA ta Duniya ta bada umarni a shawo kan wannan rigima inda tayi barazanar dakatar da Najeriya daga buga wasanni a Duniya idan har ta saba wannan umarni. FIFA tace dole Giwa ya bar ofishin NFF.

KU KARANTA: Yadda aka kashe tsohon Shugaban Najeriya a 1976

Yanzu haka dai ‘Yan kwallon mata na Najeriya su na buga Gasar U-20 na Duniya kuma za a ba su damar su karasa gasar. Sai dai bayan nan idan Gwamnati ba ta maida Amaju Pinnick kan kujerar sa ba za a iya samun babbar matsala.

Hukumar FIFA ba ta son ganin Gwamnati ta shiga cikin harkar kwallon kafa. Kwanaki dai Ministan wasannin Najeriya ya aikawa Hukumar NFF takarda inda yace Kotu ta nemi Amaju Pinnick ya sauka daga kan kujerar sa.

Hukumar kwallon ta Duniya dai ta gargadi Kasar Ghana ita ma inda tace za a hana Kasar buga wasanni idan ba ta bi ka’idar da FIFA ta gindaya ba. Katsalandan din Gwamnati a harkar wasanni ya saba layin doka na 14 da 19 na FIFA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel