Ba mu yi wa Shugaba Buhari mubaya’a ba Inji ‘Daliban Jihar Sokoto

Ba mu yi wa Shugaba Buhari mubaya’a ba Inji ‘Daliban Jihar Sokoto

Yayin da zaben 2019 ke karasowa, mun samu labari cewa wata Kungiya ta ‘Daliban Jihar Sokoto da ke karatu a fadin Najeriya sun bayyana cewa ba su yi wa wani ‘Dan takara ko wata Jam’iyya a kaf Kasar nan mubaya’a ba.

Ba mu yi wa Shugaba Buhari mubaya’a ba Inji ‘Daliban Jihar Sokoto

FOSSOSA ta karyata cewa ta nemi a zabi Wammako

Daily Trust ta rahoto cewa Kungiyar FOSSOSA ta ‘Daliban Jihar Sokoto ta musanya cewa tana tare da Shugaba Buhari da Wammako a zabe mai zuwa. Shugaban Kungiyar Kwamared Abubakar Basakwace ya karyata rade-radin da ake ji.

Abubakar Basakwace yayi jawabi a gaban ‘Yan jarida kwanan nan inda ya tabbatar da cewa Kungiyar su ba tara marawa kowa baya a zaben 2019 da za ayi. Bassakwace yace Kungiyar ta su ba ta siyasa bace kamar yadda ake nema a raya.

KU KARANTA: Inyamurai su na da wasu bukatu wajen Shugaba Buhari

A kwanakin baya an ji kishin-kishin din cewa ‘Daliban Jihar da ke lemar FOSSOSA sun ce ya zama dole a zabi Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari a 2019 domin cigaban Matasan Yankin. Kungiyar ta karyata wannan labari maras tushe.

Bassakkwace ya kara da cewa ba su ce a zabi Shugaba Muhammadu Buhari ko kuma Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aliyu Wamakko na APC a zabe mai zuwa ba domin karatu yake gaban su ba shiga cikin lamarin siyasa ba.

Dazu kun ji cewa Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana yadda zaben 2019 zai kasance. Tinubu yace kato-bayan-kato za a tsaya a fitar da ‘Yan takarar APC da su rike masu tuta a babban zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel