Zuba hannun jari: Yan kasuwar Turkiyya zasu kafa matatar man fetir a Najeriya

Zuba hannun jari: Yan kasuwar Turkiyya zasu kafa matatar man fetir a Najeriya

Hukumar kula da harkokin man fetir ta kasa, NNPC ta sanar da cewa wasu masu zuba hannun jari yan kasar Turkiyya zasu gina katafaren kamfanin matatar man fetir dake tace gangan mai dubu dari a Najeriya, inji rahoton The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban sashin ganawa da jama’a, ndu Ughumadu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 14 ga watan Agusta, inda yace tuni yan kasuwar suka fara shirye shiryen dawo da kamfanin daga kasar Turkiyya.

KU KARANTA: Inyamurai sun dingaya ma Buhari sharudddan samun goyon bayansu a zaben shekarar 2019

Zuba hannun jari: Yan kasuwar Turkiyya zasu kafa matatar man fetir a Najeriya

Matatar mai

“Wasu yan kasuwa sun fara shirin dawo da kamfanin matatar man fetir daga kasar Turkiyya, a bayan matatar mallaki kamfanin man fetir na Birtaniya ne, amma dayake sun sayar da shi, hakan ya sa yan kasuwar suke shirin dawo da shi Najeriya, a garin Fatakwal.” Inji shi.

Baya ga matatar mai ta yan kasuwa, ita ma gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar NNPC a bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kammala shirye shiryen gina sabbin kamfanuwan tace man fetir guda biyu.

Shugaban NNPC, Maikanti Baru yace guda cikin matatun za’a gina shi ne a garin Warri na jihar Delta, yayin da aiki yayi nisa a ginin sabon matatar mai da gwamnati ke yi a garin Fatakwal na jihar Ribas.

Daga karshe Baru yace bukatar NNPC shine ta fadada matatun mai dake Najeriya, tun daga na gwamnati har zuwa na yan kasuwa, sai dai bai sanar da zuwa lokacin da za’a kammala ayyukan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel