Yadda za mu yi zaben 2019 a Jam’iyyar APC - Tinubu ya gama magana

Yadda za mu yi zaben 2019 a Jam’iyyar APC - Tinubu ya gama magana

Babban jigo a Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana yadda zaben 2019 zai kasance. Tinubu yace kato-bayan-kato za a tsaya a fitar da ‘Yan takarar APC da za su rike tuta a babban zabe mai zuwa.

Yadda za mu yi zaben 2019 a Jam’iyyar APC - Tinubu ya gama magana

APC za tayi zaben fitar da gwani kato-bayan-kato a Najeriya

Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa Bola Tinubu yace Jam’iyyar su ta APC ba za ta yi amfani da tsarin da aka saba a da ba wajen fitar da ‘Yan takarar ta a zabe mai zuwa. A kan yi amfani ne da masu tsaida ‘Yan takara a baya.

Wannan karo, Asiwaju Bola Tinubu yace za a fito ne kowane ‘Dan Jam’iyya ya bi layi ya zabi ‘Dan takarar sa wajen zaben Shugaban Kasa da sauran zabuka na 2019. Tinubu yace a 2019 ba za ayi amfani da ‘Delegates’ ba.

KU KARANTA: Abin da ya kai ni wurin Obasanjo - Dankwambo

A irin wannan tsari ne aka tsaida ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Osun inda kowa ya fito ya bi layi aka zabi wanda zai rike tutar Jam’iyyar APC a zaben da za ayi bana. Tinubu yayi wannan jawabi ne da ya gana da ‘Yan APC a Legas.

Bola Tinubu ya nemi ‘Ya ‘yan APC mai mulki da su yi rajistar sunan su sannan kuma su shiryawa irin wannan sabon tsari na zaben fitar da gwani wanda Talakawa za su amfana. Tinubu ya taya APC murna lashe zabukan Bauchi da Katsina.

Tsohon Gwamnan ya kuma ce babu rikici a Jam’iyyar a Jihar Legas kamar yadda wasu ke fada. Tinubu yace su na bayan Gwamnatin Buhari 100-bisa-100 inda shi ma Gwamnan Legas ya yabawa kokarin da Jagoran na Jam’iyyar APC ya ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel