Inyamurai sun gindaya ma Buhari sharudddan samun goyon bayansu a zaben shekarar 2019

Inyamurai sun gindaya ma Buhari sharudddan samun goyon bayansu a zaben shekarar 2019

Shuwagabannin kabilar Ibo masu tunani da hangen nesa sun mika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kokon bararsu game da wata bukata daya tilo da suke bukatar shugaban ya cika musu, idan har yana neman goyon bayansu a takararsa ta yin tazarce.

Daily Trust ta ruwaito kungiyar ta bukaci Buhari ya shirya taron kasa da zata kirkiro ma Najeriya, sabon kundin tsarin mulki kafin zaben shekarar 2019, wannan ne kadai matakin da Buhari zai dauka matukar yana son ya samu kuri’un Inyamurai, a cewarsu.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Inyamurai sun dingaya ma Buhari sharudddan samun goyon bayansu a zaben shekarar 2019

Inyamurai

Kungiyar ta sanar da haka ne a ranar Talata, 14 ga watan Agusta a garin Enugu bayan wani babban taro da ta kira na yayanta, inda tace hakan ya dace ne tunda dai yan Najeriya sun yi watsi da kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Kungiyar tace matsalar dake tattare da kundin tsarin mulki na shekarar 2019 zai cigaba da shafar zabukan kasar nan idan har ba’ay kawar da shi ba, kamar yadda mjiyar Legit.ng ta ruwaito

Bugu da kari kungiyar ta nuna bacin ranta bisa yawaitan kashe kashe da zubar da jini a Najeriya, wanda yace hakan ya nuna Najeriya ta gaza, sa’annan ta yi kira ga gwamnatin tarayya data dauki matakan kawo kashe kashen.

Daga karshe kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soke haramcin da gwamnati ta dauka akan kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara, IPOB, saboda a cewarta IPOB basa daukan makamai, “Zanga zanga kawai suke yi, kuma suna da yancin yin hakan a dokar kasa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel