Cutar Gudawa ta Tsinkewa Mutane 400, ta kar 28 a Jihar Kano

Cutar Gudawa ta Tsinkewa Mutane 400, ta kar 28 a Jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, cutar gudawa ta tsinkewa Mutane 400 a tsakanin watan Janairu da Yulin wannan shekara da ta salwantar da rayukan mutane 28 cikin kananan hukumomi 33 dake fadin jihar Kano a Arewacin Kasar nan ta Najeriya.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso, shine ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata tare da bayar da tabbacin cutar Amai gami da Gudawa da cafke Mutane 50 a tsakanin watanni bakwai da suka shude.

A cewar sa, gwamnatin jihar da sanadin ma'aikatar sa ta Lafiya ta zabura wajen daukar muhimman matakai domin tunkarar wannan annoba da ta kunno kai cikin wasu jihohi 17 dake fadin Najeriya da ta hadar har da jihar Kano.

Getso yake cewa, an tanadi kimanin Naira Miliyan 32 domin yakar wannan annoba tare da hadin gwiwar kungiyar agajin gaggawa da take ci gaba da kai komo wajen laluben lunguna da sako da cutar ta fi yaduwa.

Cutar Gudawa ta Tsinkewa Mutane 400, ta kar 28 a Jihar Kano

Cutar Gudawa ta Tsinkewa Mutane 400, ta kar 28 a Jihar Kano

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Getso ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai cikin shirin nan na kawo karshen barkewar cututtuka a jihar inda ya ce wannan lamari bai takaita ga rataya wuyan gwamnatin jihar kadai ba.

KARANTA KUMA: Kotu ta watsar da Zargin Kisan gillan kan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas

Babban Likitan ya ci gaba da cewa, ya kamata cibiyoyi, kungiyoyi da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki wajen bayar da kariya da kuma kulawa da lafiyar al'umma akan su tashi tsaye domin tunkarar wannan mummunar annoba da take ke kaiwa ta kwantar.

Kazalika, Kwamishinan ya kuma shawarci al'umma kan daukan dabi'u na amfani da tsaftataccen ruwa wajen gudanar da mu'amalan su, yawaita wanke hannaye da sabulu kuma akan kari, da kuma kauracewa bayan gari a ko ina gami da sauran hanyoyi bayar da kariya ga lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel