Wani makiyin addinin musulunci ya kutsa kai da mota cikin masallacin juma'a

Wani makiyin addinin musulunci ya kutsa kai da mota cikin masallacin juma'a

Ba wannan ne karo na farko da mutane suke nuna kyamar su ga addinin musulunci ba, addinin yana samun kalubale da yawa musamman ma ta yankin nahiyar turai.

Wani makiyin addinin musulunci ya kutsa kai da mota cikin masallacin juma'a

Wani makiyin addinin musulunci ya kutsa kai da mota cikin masallacin juma'a

A wani gari mai suna Lille dake kasar Faransa wani direban mota wanda yake kyamar addinin musulunci ya kutsa kai cikin wani babban masallacin juma’a bayan an idar da sallar magariba.

Mutumin ya samu damar shiga da motar ne bayan ya karya kofar shiga masallacin. Bayanai sun nuna cewar babu mutum ko daya da mutu ko yaji ciwo, amma kuma yayi sanadiyyar asarar dukiya mai yawa a masallacin.

DUBA WANNAN: Bafarawa: Koda na fadi zaben fidda gwani bazan bar PDP ba

Wasu mutane sunce, da ace mutumin ya shiga da motar mintuna goma kafin lokacin da ya saka kai to da lamarin sai ya munana.

A halin yanzu dai hukumar tsaro ta kasar na neman mutumin, wanda ya gudu bayan ya kai harin.

Ana zaton cewar mutumin dan asalin yankin arewacin Afirka ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel