Dalilin da yasa na kai ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo – Inji Dankwambo

Dalilin da yasa na kai ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo – Inji Dankwambo

Gwamnan jihar Gombe, kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana dalilin da yasa shi kai ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa dake garin Otta na jihar Ogun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dankwambo yana cewa ya kai ziyara ga Obasanjo ne a matsayinsa na Dan halas, wanda ya kai ma Ubansa na kirki gaisuwa, dama Dankwambo ya rike mukamin babban akantan Najeriya a zamanin mulkin Obasanjo.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Sai dai Dankwambo bai bayyana ma yan jaridu batutuwan da suka tattauna da Obasanjo ba, amma ya gana da shuwagabannin jam’iyyar PDP na jihar Ogun inda ya bayyana musu manufarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Dalilin da yasa na kai ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo – Inji Dankwambo

Dankwambo a gidan Obasanjo

Da yake ganawa da shuwagabannin na PDP, Dankwambo yace idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai kaddamar da yaki akan fatara da talauci, tare da yakar zalunci da rashin adalci, sai dai yace ba zai iya kai Najeriya tudun mun tsira shi kadai ba.

“Ban taba sanin akwai ramukan kan hanya a jihar Ogun ba, saboda bamu da ramukan hanya a jihar Gombe, kunga muna ta ihun Canji muke so, amma bamu san hanyar da za’a kawo mana Canjin ba, amma na da yakinin PDP za ta yi nasara a zaben 2019.” Inji shi.

Daga karshe Dankwambo yayi alkawarin zai gudanar da ingantaccen mulki idan aka zabe shi shugaban kasar Najeriya, bugu da kari zai habbaka tattalin arzikin kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel