An yi na farko an yi na karshe: Ba zan sake barin PDP ba ko me zai faru Inji Atiku

An yi na farko an yi na karshe: Ba zan sake barin PDP ba ko me zai faru Inji Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya shiga Jihar Benin a yau Talata dinnan inda ya bayyana cewa ba fa ya matsu bane ya mulki kasar nan kamar yadda wasu ke tunani.

An yi na farko an yi na karshe: Ba zan sake barin PDP ba ko me zai faru Inji Atiku

Jirgin yakin neman zaben Atiku ya shiga kasar Benin

Alhaji Atiku Abubakar ya shiga Garin Benin a ranar nan inda bayan yayi magana da ‘Yan jarida bayan saukan sa. Atiku ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ya kamata jama’ar Najeriya su san cewa ba ido rufe yake neman Shugaban kasa ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar yake cewa da ace ya matsa sai yayi mulki, da ya zama Shugaban kasa a 2003 lokacin yana tare da Obasanjo. Atiku yace haka kuma saboda maslahar mutanen Najeriya ya janyewa Abiola takara a 1993.

KU KARANTA: Kasashen Duniya ba su son Buhari ya zarce a 2019

Atiku ya isa Garin Benin ne a wani jirgin sa tare da Sarkin yakin neman zaben sa a 2019 watau Otunba Gbenga Daniel. Atiku yana kokarin ganin ya samu goyon bayan mutanen Jihar Edo a zaben Jam’iyyar adawa ta PDP da za ayi kwanan nan.

Atiku yace in dai maganar takarar Shugaban kasa ce, babu laifi don ya sake jarraba sa’ar sa don kuwa ya cancanci ya mulki kasar nan idan aka duba, ya kuma bayyana cewa ko da bai samu tikitin PDP ba, babu abin da zai sa ya bar Jam’iyyar.

Atiku yace in dai maganar takarar Shugaban kasa ce, bai sa mulkin Kasar nan a kan sa ba inda ya kuma bayyana cewa ko da bai samu tikitin jam’iyyar PDP ba, babu abin da zai sa ya bar Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel