Yadda aka razana Akpabio don ya koma APC - Lamido

Yadda aka razana Akpabio don ya koma APC - Lamido

Babban jigon jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio ya sauya sheka ne saboda yana tsoro.

Lamido wanda ke takarar kujerar shgabancin kasa a zabe mai zuwa ya bayyana hakan a ranar Talata, 14 ga watan Agusta.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa yace Akpabio ya sauya sheka zuwa APC ne domin samun kariya kan zargin cewa gwamnatin APC ta nunawa sanatan wasu takardu sai ya tsorata.

Yadda aka razana Akpabio don ya koma APC - Lamido

Yadda aka razana Akpabio don ya koma APC - Lamido

Yace abun kunya ne yadda APC ta yiwa Akpabio tarba irin wannan cewa dama babu gaskiya a yaki da rashawarta.

KU KARANTA KUMA: Babban sakataren gwamnati yayi hasashen nasarar Buhari a zaben 2019

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kayar da dukkanin yan adawansa a zaben 2019.

Mustapha ya bayyana hakan a wata sanarwa daga Mista Lawrence Ojabo, daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya a ranar Talata a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel