Bango ya tsage: Sule Lamido yace ba zasu lamunci canza ma jam’iyyar PDP suna don wasu ba

Bango ya tsage: Sule Lamido yace ba zasu lamunci canza ma jam’iyyar PDP suna don wasu ba

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tsohon gwamna jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa ba zasu bari a canza ma jam’iyyar PDP suna ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sule Lamido ya bayyana haka ne a ranar Talata, 14 ga watan Agusta a lokacin da yake ganawa da daliget da zasu kada kuri’a a babban taron jam’iyyar da za’ayi a watan gobe.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Hukumar INEC ta kara wa’adin sati 2 don yin rajistan zabe

Lamido yace ba ire irensu da suka kafa jam’iyyar ba zasu zura idanu a canza ma PDP suna ba don kawai a faranta ma wasu da suka dawo jam’iyyar rai, don haka yace duk wanda baya son sunan PDP yana da ikon ficewa daga jam’iyyar.

Bango ya tsage: Sule Lamido yace ba zasu lamunci canza ma jam’iyyar PDP suna don wasu ba

Sule Lamido

“Jam’iyyar PDP ce kadai jam’iyyar da har yanzu take da manufa, saboda tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu jam’iyyu da dama sun canza sunayensu duk don kokarin kwatar mulki a hannun PDP, don haka ba’a canza ma tuwo suna.” Inji shi.

Dayake tsokaci kan ficewa babban dan jam’iyyar PDP, Godswill Akpabio zuwa APC, yace Akpabio ya sauya sheka ne saboda yane neman kariya tun bayan da gwamanatin APC ta nuna masa wasu muhimman takardu, sai ya razana, wannan ne ya sanya shi komawa APC.

“Abin kunya ne ga APC game da yadda suka tarbi Sanata Akpabio zuwa jam’iyyarsu, wannan ya nuna gwamnatin bata shirya yakar cin hanci da rashawa ba.” Inji Lamido.

Daga karshe tsohon gwamnan ya danganta nasarar da APC ta samu a zabukan cike gurbi da hukumar zabe ta gudanar a jihohin Bauchi, Katsina da Kogi ga magudin zabe tare da raba kudi da APC ta yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel