Kotu ta watsar da Zargin Kisan gillan kan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas

Kotu ta watsar da Zargin Kisan gillan kan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wata babbar kotun jiha dake zaman ta a garin Legas, ta yi watsi da tuhumar kisan gilla dake kan Mista Moshood Salvador, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas.

An garkame Salvador a gidan Kaso na Kirikiri tare da wasu mutane goma bisa hukuncin wata kotun majistire dake garin Yaba kan zargin su da kulla tuggun kisan gilla a ranar 25 ga watan Yuli.

A yayin zartar da hukuncin sa a ranar Talatar da ta gabata, Alkali Obafemi Adamson, ya yanke wannan sabon hukunci ne bayan sauraron shaidu gami da hujjojin lauyoyin dangane da kalubalantar tsohon hukuncin da aka zartar kan shugaban jam'iyyar.

Kotu ta watsar da Zargin Kisan gillan kan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas

Kotu ta watsar da Zargin Kisan gillan kan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas

Cikin hukuncin da Alkali Adamson ya zartar ya bayyana cewa, a sakamakon umarni gami da shawarwari na cibiyar shari'a ta jihar na bukatar wanke shugaban jam'iyyar daga laifin sa, ya sanya ya yanke hukuncin sallamar sa cikin gaggawa da gidan kaso na Kirikiri.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Fadar Shugaban 'Kasa ta Bugi 'Kirji

Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin Salvador tare da wasu mutane goma da kulla tuggun kisan Mista Adeniyi Aborishade, shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Apapa dake jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe Aborishade ne a ranar 21 ga wata Yuli yayin wani taron jam'iyyar da aka gudanar a kauyen Igbosuke dake karamar hukumar Eti-Osa, wanda wannan laidi ya sabawa sashe na 223 da kuma 233 na dokokin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel