Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ya sauya ma rundunar Yansandan nan ta musamman da tayi kaurin suna dake yaki da fashi da makami, SARS zuwa FARSA, kamar yadda mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya umarce shi.

Legit.ng ta ruwaito Sufetan ya sanar da haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 14 ga watan Agusta, inda yace daga yanzu rundunar SARS (Special Anti-Robbery Squad) ta koma FARS (Federal Anti-Robbery Squad).

KU KARANTA: Da dumi dumi: Hukumar INEC ta kara wa’adin sati 2 don yin rajistan zabe

Ranar Talatar ne Osinbajo ya umarci Babban sufetan Yansanda, Ibrahim Idris da ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS, inda ya bukaci tabbatar da duk rundunar da aka samar ta kebance kanta wajen yaki da masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makami.

Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Jami'an SARS

Daga cikin garambawul da Babban sufetan Yansanda yayi ma rundunar FARS sun hada da gwajin lafiyar jam’ian rundunar, samar da sabbin kayan sawa mai dauke da kowani jami’in FARS, hana jami’a FARS tare motoci, horas da jami’an FARS game da sabon jadawalin aikinsu.

Daga karshe Babban sufetan yace ya nada babban jami’in Dansanda mai mukamin kwamishinan Yansanda wanda zai jagoranci sabuwar rundunar ta FARS.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel