Yansanda sun cafke wasu kasurguman barayin mutane da suka sace wani babban Basarake

Yansanda sun cafke wasu kasurguman barayin mutane da suka sace wani babban Basarake

Rundunar Yansandan jihar Kogi ya sanar da kama wasu gungun yan fashi da makami da suka taba sace wani babban Basaraken jihar, Sarkin Jakura, Usman Adogah akan hanyar Kogi zuwa Okene.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ne ya sanar da haka a ranar Talata, 14 ga watan Agusta a shelwaktar Yansandan jihar a lokacin da suke bayyana ma manema labarum miyagun mutanen.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya bayyana babban musabbabin mutuwar aure a tsakanin Musulmi

Dayake bayyana yadda aka sace shi, Sarki Usman yace yana kan hanyarsa ta dawowa daga Jakura zuwa Lokoja ne yan fashin suka tare shi tare da Dansa dake jan motar da suke ciki.

Sarkin yace bayan yan fashin sun fahimci ba zasu tsaya bane, sai suka bude musu wuta, wanda hakan yayi sanadin mutuwar Dan nasa, daga nan kuma suka yi gaba da Sarkin, inda ya kwashe tsawon kwanaki biyar a hannunsu.

Daga karshe Kwamishina Ali Janga ya tabbatar ma al’ummar jihar Kogi cewa rundunar Yansandan jihar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayukan al’ummar jihar da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel