Gyara kayanka: Hukumar FIFA ta Duniya ta gindaya sharadin korar Najeriya daga harkar kwallo

Gyara kayanka: Hukumar FIFA ta Duniya ta gindaya sharadin korar Najeriya daga harkar kwallo

Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, ta yi barazanar fatattakar Najeriya daga harkar kwallon kafa matukar gwamnatin Najeriya ba ta bi sharadin data gindaya mata ba, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito FIFA tace ta samu labarin bahallatsar dake faruwa a hukumar kwallon kafa ta Najeriya game da shugabanci, tare da shishshigin da gwamnatin Najeriya ke yi a harkar hukumar kwallon.

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake sun sabbaba mutuwar mutane 10 a Madagali

FIFA ta umarcu gwmanatin Najeriya da duk masu hannu cikin wannan rikita rikita dasu tabbata shugaban hukumar Amaju Pinnick ya koma kan kujerarsa zuwa ranar Litinin, 20 ga watan Agusta, ko kuma Najeriya ta fuskanci sallama daga harkar kwallon kafa.

A yan kwanakin da suka gabata ne dai wata kotu dake zamanta a garin Jos na jihar Filato ta kwace shugabancin NFF daga hannun Amaju Pinnick ta mika shi ga Chris Giwa, wanda tace shine halastaccen shugaban hukumar.

FIFA tace idan har ta buga ma Najeriya sanda, toh ba zata dage shu ba har sai Amaju Pinnick da sakatarensa Mohammed Sunusi sun tabbatar mata an mika musu ragamar tafiyar da hukumar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel