Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Fadar Shugaban 'Kasa ta Bugi 'Kirji

Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Fadar Shugaban 'Kasa ta Bugi 'Kirji

Za ku ji cewa fadar shugaban kasa ta kyautata zato tarea kyautata tsammanin ta dangane da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 duba da nasarar a jam'iyyar APC ta yi a ranar Litinin din da ta gabata a zabukan maye gurbi na 'yan Majalisar tarayya.

Fadar shugaban kasar ta yi bugun gaba tare da cewar ba bu shakka shugaba Buhari zai yi nasara tare da lashe zaben 2019 sakamakon nasarar da jam'iyyar sa ta APC ta samu a zabukan maye gurbi da aka gudanar cikin wasu jihohi a karshen makon da ya gabata na kujerun 'yan majalisu.

Babban hadimi na musamman ga shugaban kasar akan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema na fadar shugaban kasar dake babban birnin tarayya ta Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta bayar da sanarwar nasarorin da jam'iyyar APC tayi a zabukan maye gurbin kujerun wasu sanatoci da aka gudanar a jihohin Katsina, Bauchi, da kuma Kogi a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Fadar Shugaban 'Kasa ta Bugi 'Kirji

Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Fadar Shugaban 'Kasa ta Bugi 'Kirji

Shehu yake cewa, nasarorin sun biyo bayan nasarar da jam'iyyar APC ta yi a zaben gwamna na jihar Ekiti da aka gudanar a kwana-kwanan nan, wanda hausawa ke cewa Juma'ar da za tayi kyau tun Laraba ake ganewa da hakan yake haskaka nasarar jam'iyyar a babban zabe na 2019 mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Wata Babbar Mota ta muƙurƙushe Motoci 15 a Babbar Hanyar garin Keffi zuwa Abuja

Ya ci gaba da cewa, nasarorin sun tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun kai makura tare da tura da ta kai bango dangane da tsarin mulki na jam'iyyar adawa ta PDP. Kuma nasarori alamu ne dake bayyana wasa da hankali da majalisar dokoki ta tarayya ke yiwa al'ummar kasar nan.

Kakakin shugaban kasar ya kuma nemi mambobin majalisar tarayya akan goyon bayan shugaban kasa Buhari wajen tabbatar kudiri gami da alkawurran da ya dauka yayin yakin neman zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel