Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Makarfi

Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Makarfi

Tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Demokratic Party na rikon kwarya kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ta PDP, Ahmed Makarfi ya bayyana cewa lallai idan har ya lashe zaben shugabancin kasar Najeriya zai canza fasalin al’amuran kasar.

Makarfi ya yi wannan furuci ne a garin Asaba, babban birnin jihar Delta yayin da ya kai ziyarar ganawa da neman amincewar wakilan jam’iyyar na son takara a zabe mai zuwa.

Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Makarfi

Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Makarfi
Source: Depositphotos

Makarfi ya jadadda cewa abu na farko da zai mayar da hankali wajen aiwatarwa shine sake fasalin lamuran kasar, cewa za a ba kowani yanki a kasar nan dama ta yadda ba za a sami wani bangare da zai na korafin ana muzguna masa ba ko kuma nuna masa wariya.

KU KARANTA KUMA: Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Ya roki wakilan jam’iyyar da su tabbata sun zabi dan takarar da zai fidda jam’iyyar daga kunya.

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya jinjina wa Makarfi sannan ya ce tabbas dan takara ne da ya san halin da kasa ke ciki, sannan kuma mutum ne da ke da gaskiya a al’amurran sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel