Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayar da umurnin yiwa sashin SARS na 'yan sanda garambawul cikin gaggawa

Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayar da umurnin yiwa sashin SARS na 'yan sanda garambawul cikin gaggawa

Mukadashin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bawa Sufeta Janar na 'yan sandan na kasa, Ibrahim Idris, umurnin gudanar da bincike tare da yin canji a ma'aikata da shugabanin 'yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami da akafi sani da SARS.

Legit.ng ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na fannin kafafen yadda labarai, Bashir Ahmad ne ya bayar da sanarwar a shafinsa na Twitter a ranar 14 ga watan Augustan 2018.

Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayar da umurnin yiwa sashin SARS na 'yan sanda garambawul cikin gaggawa

Yanzu-Yanzu: Osinbajo ya bayar da umurnin yiwa sashin SARS na 'yan sanda garambawul cikin gaggawa

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden daloli da Kwankwaso ya boye a Ukraine

Yace: "Mukadashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar da umurnin yin garambawul ga 'yan hukumar 'yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami (SARS) ba tare da bata lokaci ba."

Osinbajo yace daukan wannnan matakin ya zama dole saboda irin rahotanni cin zarafin mutane da keta hakkin bil-adama da mutane da dama ke yi game da ayyukan hukumar. Ya zama dole a tabbatar cewa dukkan aikin ma'aikatan hukumar sun cancanta da gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel