Dole Bukola Saraki ya bar majalisa — Akpabio

Dole Bukola Saraki ya bar majalisa — Akpabio

Tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya ce dole shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya bar majalisar idan har ana so a kore shi (Akpabio) daga majalisar.

Sanata Akpabio, wanda ya bar mukaminsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar a lokacin da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, ya bayyana hakan a yayinda yake zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

Saraki ya bi sawun wasu sanatoci da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mara rinjaye lamarin da ya sa jam'iyyar APC mai rinjaye ke cewa ya kamata ya sauka daga shugabancin majalisar.\

Dole Bukola Saraki ya bar majalisa — Akpabio

Dole Bukola Saraki ya bar majalisa — Akpabio

Akpabio yace idan har wasu suna neman a ayyana cewar babu kowa kujerar mazabarsa a majalisar saboda ya koma APC, dole Saraki da wadanda suka bar APC su ma su bar kujerunsu a majalisar.

KU KARANTA KUMA: Ku daina aron kudi domin yanka ragon layya – Kungiyar kare hakkin Musulmi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, sannan kuma daya daga cikin masu neman tikitin kujerar shugabancin kasar nan karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, yace ba zai bar jam'iyyar ba koda ya sha kaye a zaben fidda gwani.

Yace yana nan daram a PDP koda ba shi aka tsayar a neman shugabancin kasar ba, ra'ayin al'umma ne farko. Yace kowacce gasa akwai mai nasara da kuma wanda zai fadi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel