APC na bukatar ‘Yan Majalisa 73 kafin ta iya tsige Saraki inji Lauyoyi

APC na bukatar ‘Yan Majalisa 73 kafin ta iya tsige Saraki inji Lauyoyi

- Lauyoyi irin su Femi Falana sun yi magana game da batun Bukola Saraki

- Falana SAN ya nemi APC ta maida wukar sauke Saraki daga kujerar sa

APC na bukatar ‘Yan Majalisa 73 kafin ta iya tsige Saraki inji Lauyoyi

Lauyoyi sun bayyana abin da doka ta ce game da batun Saraki

Mun samu labari cewa an bayyana yadda za a iya tsige Bukola Saraki daga mukamin sa. Yanzu haka dai Jam’iyyar APC mai mulki ta huro wuta cewa Shugaban Majalisar Dattawan yayi murabus. APC tace ta ma dai fara shirin sauke Saraki.

Wani fitaccen Lauya a kasar nan Femi Falana ya nemu Jam’iyyar APC ta hakura da maganar tsige Bukola Saraki daga kujerar sa. Manyan Lauyoyin kasar irin Mike Ozekhome SAN sun sa bakin su game da shirin da ake yin a tsige Saraki.

KU KARANTA: Ana nema Kotu ta hana a tsige Saraki a Majalisa

Wadanda su ka fahimci harkar shari’a sun bayyana cewa tsarin mulkin kasa ya tanadi cewa dole APC ta samu ‘Yan Majalisa akalla 73 idan har ta na so ta tsige Bukola Saraki daga kujerar sa na Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.

Wasu Lauyoyin su na ikirarin cewa Saraki zai bar kujerar sa idan har ‘Yan Majalisu 24 su ka sa hannu cewa ya sauka daga mukamin na sa. Manyan Lauyoyin da su ka san harkar shari’a sun ce sam babu gaskiya a wannan magana da ake yi.

Femi Falana SAN ya nemi Jam’iyyar APC ta maida wukar da ta zaro na sauke Saraki daga kujerar sa a lokacin da yayi hira da Jaridar Sun. Jam’iyyar APC mai mulki tace tun da Saraki ya koma PDP, dole yayi murabus inda shi kuma yace a-ta-fau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel