Hukumar INEC ba za ta iya gudanar da zaben kwarai ba – Inji PDP

Hukumar INEC ba za ta iya gudanar da zaben kwarai ba – Inji PDP

Mun samu labari cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta nuna shakkun ta game da Hukumar zabe na kasa watau INEC inda tace Hukumar ba za ta iya shiryawa Najeriya zabe mai inganci a 2019 ba.

Hukumar INEC ba za ta iya gudanar da zaben kwarai ba – Inji PDP

PDP tace INEC ba za ta iya yin zaben gaskiya a 2019 ba

Jam’iyyar PDP tayi wannan magana ne bayan da aka samu dinbin katin zabe na PVC a gidan tsohon Shugaban Hukumar DSS na kasa. Sakataren yada labarai na PDP yace hakan na nuna cewa zai yi wuya ayi zaben adalci a shekarar badi.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne Sakataren yada labarai na babbar Jam’iyyar adawar kasar yace abin da ke faruwa a Najeriya ya tabbatar da cewa zai yi wahala INEC ta yi zabe na gaskiya da gaskiya a 2019 kuma tun da wuri gara INEC tayi bayani.

KU KARANTA: Zaben Daura: Ba za mu amince da sakamakon INEC ba – Inji PDP

Jam’iyyar adawar tace akwai kuma alaka ta-jini mai girma tsakanin wata babbar Jami’ar INEC da Shugaban kasa Buhari wanda kowa ya san da wannan. Wadannan dalilai dai sun sa Jam;iyyar PDP tana ganin cewa ba za ayi adalci a zaben 2019 ba.

Za ku ji cewa an zargi wasu manyan Gwamnoni na Jam’iyyar APC mai mulki da kashe makudan kudi domin sayen kuri’un Talakawa a zaben Sanatan da aka yi kwanan nan a Jihar Bauchi. Ana zargin APC ta batar da sama da Biliyan 2 a kan zaben.

Ana jin kishin-kishin din cewa an samu wasu katin zabe na PVC da kudi a gidan tsohon Shugaban DSS da aka sallama daga aiki watau Lawal Daura. Hukumar DSS ta karyata wannan rade-radi dai tuni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel