Karo na biyu, Buhari ya yi watsi da dokar sauya fasalin zabe da majalisa ta gabatar

Karo na biyu, Buhari ya yi watsi da dokar sauya fasalin zabe da majalisa ta gabatar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake kin amincewa da kudirin sake fasali ga Dokar Zabe ta 2018, inda ya kawo dalilansa, wanda yake cewa sake faalin na iya canja tsari da ka’idar aikin zabe na kasar.

A cewar shugaban kasar ga shugaban majalisar dattawa ta kasar Dr. Bukola Saraki, da kuma kakakin majalisar wakilan tarayya Hon. Yakubu Dogara, kamar yadda jaridar THISDAY ta ruwaito, wasu daga cikin bayanan sake fasalin dokar zasu raunana ayuukan Hukumar gudanar da Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Sai dai shugaban kasar har ila yau, tafi da kuskuren sake fasalin wanda ke nuni da kin amfani da na’urar tantance masu kada kuri’ar wato Card Reader a zaben 2019, wanda masu fashin baki kan harkokin siyasa ke ganin cewar amfani da na’urar zai sa ayi zabe wanda babu magudi a ciki.

Wanda shine dai karo na biyu da shugaban kasar yaki amincewa da sake fasalin dokar Zabe ta kasar.

KU KARANTA: Sambo Dasuki na daf da fitowa bayan sauya sabon shugaban DSS

Babban mai tallafawa shugaban kasar kan harkokin Majalisar Dokoki ta kasa, Sanata Ita Enang, ya jaddadawa jaridar THISDAY a wayar tarho cewa shugaban kasar yak i amincewa a sake fasalin dokar ne bisa wasu muhimman dalili, sai dai ya bayyana cewa an sake gabatar da wani kudiri na sake fasalin dokar zaben karo na Uku a ranar 24 ga watan Yuli, 2018, wanda har yanzu yake ajiye a teburin shugaban kasar.

“Zan gabatar da cikakken bayani gobe” a cewar sanata Enang.

A watan Mayu shugaba Buhari yayi watsi da kudirin sake fasalin dokar zabe, kudirin da zai kawo sauye sauye a tsarin gudanar da zaben 2019, inda kudirin ya sanya zaben Majalisar dokoki ta kasa a farko, wanda na shugaban kaa da majalisar dokoki ta jihohi zai zo daga karshe.

Karo na biyu, Buhari ya yi watsi da dokar sauya fasalin zabe da majalisa ta gabatar

Karo na biyu, Buhari ya yi watsi da dokar sauya fasalin zabe da majalisa ta gabatar

“Sashi na 25 na dokar, na iya sabawa da ikon gudanar da ayyukan Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, wajen tsarawa, gudanarwa da kuma sa ido kan zabe kamar yadda yake a sashe na 15 sadara ta (A) na dokar zaben”

Sai dai Yace kotun daukaka kara a wannan watan ta fitar da hukuncin cewa Majalisar dokoki ta kasa na da ikon sake fasalin gudanar da zaben kasar.

A bisa mahanga, kin amincewa da sake fasalin dokar yanzu tursasa tare da nuna rashin muhimmancin,kudirin shugaban kasar na siye da kuma dagadarajar nau’rar tantance masu kada kuri’a ga hukumar INEC wanda aka shirya yi akan Naira Biliyan 242, a kasafin gudanar da zaben 2019.

Wata Babbar Kotu ta yanke hukunci cewar duk da cewa na’urar tantance masu kada kuri’a da sauran na’uarorin gudanar da zabe zasu taimaka wajen yin sahihin zabe, Hakan dai baya kunshe a cikin kundin dokar gudanar da zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel