Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

Mahukunta a Jami'ar Gwamnatin Tarayya na Fasaha (FUT) dake Minna ta Jihar Neja sun bayar da sanarwar korar daya daga cikin malaman jami'an mai suna Omananyi Yunusa saboda samunsa da laifin neman lalata da wata dalibar jami'ar.

Mataimakin Direktan yadda labarai na jami'ar, Lydia Legbo, tace an cimma matsayar korar Mr Yunusa ne bayan an gudanar da bincike game da zargin neman lalata da wata daliba mai daukar darasin da lakcaran ke koyarwa ta shigar a hirar tarho da tayi da Premium Times.

Kafin korarsa, Mr Omananyi dai malami ne dake koyarwa a sashin nazarin duwatsu da albarkatun kasa wato Geology a turance.

Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

"Tabbas, an sallame shi daga aiki saboda laifuka masu nasaba da neman yin lalata da aka tabbatar ya aikata bayan an gudanar da bincike," inji Lydia.

DUBA WANNAN: Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

An cimma matsayar korar Mr Yunusa ne a taron mahukunta na jam'ar karo na 31 da aka gudanar karkashin jagorancin shugaban jami'ar, Abdullahi Bala bayan kwamitin bincike ta bayar da sakamakonta da ya nuna cewa malamin ya aikata laifin.

"Ba'a sanar da kafafen yadda labarai game da binciken da ake yi ba'a son hayaniya game da lamarin lokacin binciken. A gaskiya, yawancin sassa da dama na jami'ar basu san da binciken ba har sai lokacin da aka zartas da hukuncin," inji wani dalibi a jami'ar mai suna Yusuf Abideen.

Wata daliba kawar yarinyar da malamin ya nemi lalata da ita wadda ta nemi a sakayya sunanta ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa korar Mr Yunusa daga jami'ar zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ga daliban jami'ar.

Shugaban jami'ar yace wannan korar zai zama darasi ga sauran malaman jami'an masu irin wannan halin.

A ranar 20 ga watan Yulin wannan shekarar, jami'ar Obafemi Awolowo dake Ibadan itama ta kori wani lakcara mai suna Richard Akindele bayan samunsa da laifin neman kwanciya da wata daliba kafin domin ya bata maki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel