Gwamnatin Buhari ta gazawa yan Najeriya – Jerry Gana

Gwamnatin Buhari ta gazawa yan Najeriya – Jerry Gana

Tsohon jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Jerry Gana, ya kaddamar da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza samarwa yan Najeriya da tsaro, wanda shine hakki na farko da ya rataya akan gwamnati.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa Gana wadda ke takara a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party ya kaddamar da cewa yana neman takarar kujerar shugaban kasa ne ba wai saboda san ransa ba.

Gwamnatin Buhari ta gazawa yan Najeriya – Jerry Gana

Gwamnatin Buhari ta gazawa yan Najeriya – Jerry Gana

A cewarsa duk wani mai tunani a kasar ya san cewa kasar na bukatar wanda zai ceto ta daga mawuyacin halin da take ciki.

KU KARANTA KUMA: An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

Ya jadadda cewa yan Najeriya sun gaji da mulkin APC saboda haka jam’iyyar SDP ta fito domin ta ceto su da kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel