2019: Ba zan janyewa kowa ba - Gwamnan PDP dake takarar shugabancin kasa

2019: Ba zan janyewa kowa ba - Gwamnan PDP dake takarar shugabancin kasa

Gwamman jihar Gombe, Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo ya karyata labarin dake yawo a wasu kafafen yadda labarai na cewa ya janye niyyarsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2019, inda yace rahoton karya ce tsantsagoronta da ya kamata a jefa a kwandon shara.

A yayin da yake Allah wadai da rahoton, gwamna Dankwambo yace wanda suka rubuta rahoton suna son kawo rashin jituwa ne tsakaninsa da takwaransa Honarabul Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato inda suke son nuna cewa Tambuwal yafi farin jini.

2019: Ba zan janyewa kowa ba - Gwamnan PDP dake takarar shugabancin kasa

2019: Ba zan janyewa kowa ba - Gwamnan PDP dake takarar shugabancin kasa

DUBA WANNAN: Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

A sanawar da ya fitar da bakin mai taimaka masa a fannin yada labarai, Junaidu Usman, Gwamna Dankwambo ya fadi karara cewa ba zai janye takararsa saboda Gwamna Tambuwal ba ko wani daban ba domin ya fito takara ne saboda al'ummar Najeriya.

Sanarwan ta cigaba da cewa, "muna kyautata zaton cewa Dankwambo ne zai lashe zaben fidda gwani a PDP kuma al'ummar Najeriya zasu jefa masu kuri'unsu idan zaben yazo, domin wannan hanyar ce kadai yadda zamu iya ceto Najeriya daga halin da ta fada."

Gwamnan kuma yace ba abin mamaki bane gwamnoni dake abota su rika gayyatan juna wajen taron kaddamar da ayyukan da gwamnatocin su suka yiwa al'umma.

"Kusancin da ke tsakanin Dankwambo da Tambuwal har da kai ga gwamna Tambuwal ya sanyawa wata layi suna Dankwambo a babban birnin jihar Sakkwato. Saboda haka wannan kawai alama ce dake nuna cewa gwamnonin biyu suna da kyakyawar fahimta tsakaninsu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel