Hukumar INEC ta bayar da takardun shaidar dawowa ga zababbun sanatoci

Hukumar INEC ta bayar da takardun shaidar dawowa ga zababbun sanatoci

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar da takardun shaidar dawowa aiki ga zababbun sanatoci, Ahmad Kaita, (APC, Katsina Arewa) da Lawal Yahaya Gumau, (APC, Bauchi Kudu) wadanda suka lashe zabe a zaben cike gurbi da akayi a ranar Asabar.

Hukumar a wata sanarwa daga daraktan labaranta kuma mai ilimantar da masu zabe, Mista Oluwole Osaze-Uzzi, a Abuja yace dukkanin su biyu sun lashe zaben cike gurbi da akayi a mazabun su.

Bayan ya karbi takardarsa, Kaita ya godema hukumar kan yadda ta gudanar da zabe mai inganci cikin gaskiya da amana a mazabarsa.

Hukumar INEC ta bayar da takardun shaidar dawowa ga zababbun sanatoci

Hukumar INEC ta bayar da takardun shaidar dawowa ga zababbun sanatoci

Haka zalika Gumau ya bayyana zaben a matsayin mai inganci ta fannin shirye-shirye da yadda hukumar INEC da jami’anta suka gudanar da zzaben.

KU KARANTA KUMA: An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

Gumau yayi kira ga jama’a da su ci gaba da ba INEC cikakken goyon baya a zabe.

An gudanar da zabukan ne domin cike guraben sanatocin da suka mutu akan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel