Dalilin da yasa ba zamu iya dawowa majalisa ba yanzu – Saraki, Dogara

Dalilin da yasa ba zamu iya dawowa majalisa ba yanzu – Saraki, Dogara

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun bayyana cewa ba’a sa ranar dawowa majalisar dokokin kasar don duba kasafin kudin zabe 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar 17 ga watan Yulin 2018 ba.

Jawabin Saraki da Dogara dauke das a hannun hadimansu a kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu da Turaki Hassan sun bayyana cewa majalisar dokokin kasar bazata iya dawowa zama ba har sai kwamitin da aka kafa don duba kasafin kudin INEC sun samu rahoton gabatarwa.

Dalilin da yasa ba zamu iya dawowa majalisa ba yanzu – Saraki, Dogara

Dalilin da yasa ba zamu iya dawowa majalisa ba yanzu – Saraki, Dogara

Ana kuma sanya ran cewa kwamitin hadin gwiwar zasu gana da na majalisar dattawa da kwamitin majalisar wakilai kan lura da ciwo bashi inda ana za’a gabatar da rahotanni biyu a majalisun biyu.

KU KARANTA KUMA: Na ka ke bada kai: Idan na tsaya takara Inyamurai za su mani adawa - Okorocha

Sun kara da cewa ba gudanar da ganawa makamanciyar haka ba saboda haka majalisun biyu bazasu iya dawowa ba saboda babu rahoton da za’a duba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel