Canji: Farashin iskan gas na dafa abinci ya karye bayan gwamnati ta cire masa haraji

Canji: Farashin iskan gas na dafa abinci ya karye bayan gwamnati ta cire masa haraji

Alamomi dai na nuna cewa yanzu yan Najeriya musamman ma masu anfani da iskar gas din dafa abinci za su samu sauki biyo bayan farashin iskan gas din da ya sauka bayan cire harajin da gwamnatin tarayya tayi akan sa.

Masana tattalin arziki dai sun yi hasashen cewa da wannan cigaban da aka samu, yanzu ana sa ran farashin na gas din ya ragu da kusan kaso ashirin cikin dari akan farashin sa na da.

Canji: Farashin iskan gas na dafa abinci ya karye bayan gwamnati ta cire masa haraji

Canji: Farashin iskan gas na dafa abinci ya karye bayan gwamnati ta cire masa haraji

KU KARANTA: Yan APC a jihar Akwa Ibom sun ce ba su son Akpabio

Legit.ng ta samu cewa tun ba yanzu ba 'yan kasuwar dake harkar sayar da iskan gas din suna ta korafin cewa harajin da gwamnati ta sa wa iskan gas din shine musabbabin dalilin tsadar sa.

A wani labarin kuma, Kungiyar nan ta taron gwamnonin yankin Arewacin kasar nan su goma-sha-tara watau Northern States Governors’ Forum (NSGF) a turance sun sanar da tsige shugaban kamfanin cigaban Arewa watau New Nigeria Development Company (NNDC).

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima inda suka bayyana dalilai na rashin katabus daga shugaban wajen rike kamfanin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel