Da dumin sa: Shugaban kamfanin cigaban yankin Arewa ya rasa mukamin sa

Da dumin sa: Shugaban kamfanin cigaban yankin Arewa ya rasa mukamin sa

Kungiyar nan ta taron gwamnonin yankin Arewacin kasar nan su goma-sha-tara watau Northern States Governors’ Forum (NSGF) a turance sun sanar da tsige shugaban kamfanin cigaban Arewa watau New Nigeria Development Company (NNDC).

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima inda suka bayyana dalilai na rashin katabus daga shugaban wajen rike kamfanin.

Da dumin sa: Shugaban kamfanin cigaban yankin Arewa ya rasa mukamin sa

Da dumin sa: Shugaban kamfanin cigaban yankin Arewa ya rasa mukamin sa

KU KARANTA: An tsinci gawar hadimin wani gwamna a dakin sa

Legit.ng ta samu cewa shi dai babban kamfanin na cigaban arewa an kafashi ne shekaru da dama da suka gabata domin cigaban tattalin arzikin yankin amma kawo yanzu ba'a samu cimma wannan manufar ba.

A wani labarin kuma, Alamomi dai na nuna cewa yanzu yan Najeriya musamman ma masu anfani da iskar gas din dafa abinci za su samu sauki biyo bayan farashin iskan gas din da ya sauka bayan cire harajin da gwamnatin tarayya tayi akan sa.

Masana tattalin arziki dai sun yi hasashen cewa da wannan cigaban da aka samu, yanzu ana sa ran farashin na gas din ya ragu da kusan kaso ashirin cikin dari akan farashin sa na da.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel