Hankulan jama'a ya tashi bayan an sake harbe wani mutum da tsakar rana a Ado Ekiti

Hankulan jama'a ya tashi bayan an sake harbe wani mutum da tsakar rana a Ado Ekiti

- Bai wuce kwana uku ba da aka kashe Mista Bunmi Ojo wani na hannun daman tsohon gwamnan jihar

- Anyi aika aikar ne a sabuwar gadar Okesa zuwa Ojumose dake garin Ado Ekiti

Hankulan jama'a ya tashi bayan an sake harbe wani mutum da tsakar rana a Ado Ekiti

Hankulan jama'a ya tashi bayan an sake harbe wani mutum da tsakar rana a Ado Ekiti

Wani abin tsoro ya kara faruwa a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Litinin inda yan bindiga suka kashe wani mutum da tsakar rana.

Ofishin dillancin labarai sun ruwaito cewa, kisan mutumin wanda ba a san ko waye ba ya biyo bayan kashe Mista Bunmi Ojo, makusancin tsohon gwamnan jihar, Gwamna Segun Oni wanda bai wuce kwana uku ba.

DUBA WANNAN: Za'a dai-dai ta rabon gado tsakanin maza da mata

Ganau ba jiyau ba sunce an kashe mutumin ne akan sabuwar gadar Okesa zuwa Ojumose, dake garin, da misalin karfe 5:30 na yamma.

Kamar yanda wadanda suka bayyana, mutumin na kan babur din haya ne, mutanen kuma na biye dashi.

'Yan bindigar suna kan babur din haya ne suma, inda suka tsayar da matukin babur din mutumin. A take suka aika dashi lahira tare da tserewa a babur dinsu.

Tuni aka wuce da gawar mamacin asibiti.

Wannan abu ya jawo rufe shagunan dake kasuwar Bisi da kewaye.

A lokacin da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, DSP Caleb Ikechukwu, ya sanar da ofishin dillancin labarai cewa basu riga da sun samu rahoton daga hukumar yan sandan yankin Okesa ba.

Yayi alkawarin bada rahoton yana isowa garesu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel