Abin ya zafafa: Saraki sun ruga kotu, da rokon ta hana IGP, AGF da DSS tsige su, kuma ta kai musu

Abin ya zafafa: Saraki sun ruga kotu, da rokon ta hana IGP, AGF da DSS tsige su, kuma ta kai musu

- Watakila karshen sa toka sa katsin dake faruwa dangane da batun tsige shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki yazo karshe

- Yanzu haka wata babbar kotun tarayya ta bayar da kariya gare shi da wasu 'yan majalisar

Wata babbar kotun daukaka kara dake da matsuguni a birnin tarayya Abuja ta dakatar da babban mai shari'a kuma ministan Shari'a na kasa da babban Sufeton ‘yan sanda da kuma daraktan rundunar tsaron farin kaya ta kasa (DSS) daga yin dukkanin wani yunkurin taimakawa wajen tsige shugaban majalisar dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki, ta yin amfani da tanadin dokar kundin tsarin mulkin kasar nan sashe na 50 (2)(C) .

Abin ya zafafa: Saraki ya ruga kotu, ya roki ta hana IGP, AGF da DSS tsige shi

Abin ya zafafa: Saraki ya ruga kotu, ya roki ta hana IGP, AGF da DSS tsige shi

Bukatar hakan Na kunshe ne cikin karar da Sanata Rafiu Adebayo daga jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar kwara ta kudu da kuma takwaransa na mai wakiltar Bauchi ta tsakiya wato Sanata Isa Hamma Misau, da kuma tsohon mai shari'a na kasa Kanu Agabi da wani babban lauyan Mahmud Magaji SAN.

KU KARANTA: Sarkin Kano yayi lugude kan ‘yan siyasa masu ci-da-addini

Masu shigar da karar sun bayyana cewa bayan ficewar da wani bangare ya yi daga jam’iyyar APC, hakan ya sanya wasu suka kudiri aniyyar kawar da shugaban majalisar dattawa daga mukaminsa ta kowanne hali.

Sashe na 50 (2) ya fayyace cewa shugaban majalisar dattawa ko mataimakinsa, kakakin majalisar dokokin na tarayya ko mataimakinsa, za su bar kan mukaminsu ne idan har aka samu kaso biyu daga cikin uku na adadin yawan ‘yan majalisar da suka bukaci hakan".

Cikin wadanda kotun ta bayar da kariyar sun hada da shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa da Sanata Ahmed Lawan da Sanata Bala Ibn Nallah da Sanata Emma Buacha da kuma Akawun majalisar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel