Kuma dai: Bayan mutuwar ‘yan bautar kasa 9, yanzu haka wasu 19 sun tsallake rijiya da baya

Kuma dai: Bayan mutuwar ‘yan bautar kasa 9, yanzu haka wasu 19 sun tsallake rijiya da baya

- Sauran kirin a kuma sake kwata samun mummunan labari kan 'yan bautar kasa

- Wannan karon ba'a ruwa zasu nitse ba, hadarin mota ne ya rutsa da su

- Amma Allah ya kiyaye babu wanda ya mutu, sai dai 'yan raunuka

Wasu ‘yan bautar kasa a jiya Litinin su 19 sun tsallake rijiya da baya akan hanyarsu ta zuwa garin Sango-Ota.

Babbar kwamandar kiyaye hadduru ta kasa reshen jihar Ogun Florence Okpe ta bayyana cewa ‘yan bautar kasar sun yi nasarar kubuta daga hadarin da ya kusa ritsawa da su a lokacin da suka fito daga sansanin horarwa na jihar Ogun da ke Sagamu.

Kuma dai: Bayan mutuwar ‘yan bautar kasa 9, yanzu haka wasu 19 sun tsallake rijiya da baya

Kuma dai: Bayan mutuwar ‘yan bautar kasa 9, yanzu haka wasu 19 sun tsallake rijiya da baya

Hadarin ya faru ne a dai-dai kauyen Danco da ke karshen babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Florence ta kara da cewa babbar motar kirar kwasta mai cin mutane 37, ta kwace daga hannun direbanta wanda hakan ya jawo hadarin, amma ba'a samu hasarar rai ko daya ba.

KU KARANTA: Lamari yayi tsamari yayin zanga-zangar kasuwar 'yan waya ta Kano (Hotuna)

A karshe Florence ta tabbatar da cewa wadanda suka samu raunin a cikin ‘yan bautar kasar suna karamin Asibitin hukumar kula da kiyaye haddura domin karbar magani, yayin da sauran mutum hudu kuma da suka samu manyan raunika aka garzaya da su zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo dake Sagamu.

Sannan ta kara yin kira ga al'umma da su dinga kiyayewa da yin tuki musamman a lokacin da ake ruwan sama.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel