Kuji maganar da Shehu Sani yayi akan rikicin sojoji da aka yi a garin Maiduguri

Kuji maganar da Shehu Sani yayi akan rikicin sojoji da aka yi a garin Maiduguri

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yayi magana akan rikicin da aka samu tsakanin sojoji a filin tashi da saukar jirgin sama na garin Maiduguri dake jihar Borno

Kuji maganar da Shehu Sani yayi akan rikicin sojoji da aka yi a garin Maiduguri

Kuji maganar da Shehu Sani yayi akan rikicin sojoji da aka yi a garin Maiduguri

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yayi magana akan rikicin da aka samu tsakanin sojoji a filin tashi da saukar jirgin sama na garin Maiduguri dake jihar Borno.

Fusatattun sojojin sun isa filin jirgin saman da misalin karfe 6 na yamma, bayan an tura su karamar hukumar Marte dake cikin jihar ta Borno.

DUBA WANNAN: Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Shehu Sani yace irin wannan matsalar ba wata abar tada hankali bace, kuma cikin kankanin lokaci za a samu mafita, inda yayi kira ga gwamnati data dinga taimakawa sojojin tana kara musu kwarin guiwa, tunda har sun zabi su sayar da rayukan su domin tsare lafiyar al'umma da kasar nan baki daya.

Ga abinda Shehu Sani yace: "Rikicin da sojoji suka so su tada a filin jirgin sama na Maiduguri, abu ne wanda za'a iya kawo karshen shi. Dole ne mu basu gudummawa da karfin guiwa, tunda har zasu sayar da rayukan su domin su kare lafiyar mu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel