‘Yan sanda sun cafke wani Saurayi da kwarangwal din kan mutune 3

‘Yan sanda sun cafke wani Saurayi da kwarangwal din kan mutune 3

- Dubun wani dan yankan kai ta cika, ya shiga komar jami'an tsaro

- Amma sai dai bayan kama shi ya bayyana cewa shi kawai dan riko ne

- Tuni mai gidansa ya tsere yayin da yaga 'yan sanda na shirin jimma

Jami'an rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Oyo sun damke wani mutum bisa kama shi da aka yi da kokon kawunan mutane har guda 3, a birnin Ibadan a jiya Litinin.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ta Oyo Mista Abiodun Odude, ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutumin ne mai suna Sodiq Rasheed dan kimanin shekaru 27 da haihuwa a duniya a yankin Omi Adio.

‘Yan sanda sun cafke wani Saurayi da kwarangwal din kan mutune 3

‘Yan sanda sun cafke wani Saurayi da kwarangwal din kan mutune 3

Odude ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai yayin holar wanda ake zargin, inda ya kara da cewa akwai sauran laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa.

KU KARANTA: Lamari yayi tsamari yayin zanga-zangar kasuwar 'yan waya ta Kano (Hotuna)

A nasa bangaren wanda aka kama da kawunan Sodiq Rasheed, ya bayyanawa ‘yan jaridun cewa wani mutum ne ya umarce shi da aikata wannan danyen aiki.

"Wani Mutum ne ya yaudareni har na kai ga zama mai aikata laifi" In Ji Sodiq Rasheed.

“Na taya shi yin wani aiki ne, bayan da muka kammala aikin sai ya bukaci da in kawo masa kokonn kan mutane guda 3 domin yin asiri".

“Na samu nasarar samun wadannan kokunan kawunan ne a makabartar Omi Adio, inda a nan ne jami'an tsaro suka kamani yayin da shi kuma mai gidan nawa ya arce" a cewar Sodiq.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel