Na ka ke bada kai: Idan na tsaya takara Inyamurai za su mani adawa - Okorocha

Na ka ke bada kai: Idan na tsaya takara Inyamurai za su mani adawa - Okorocha

Mun samu labari daga Jarida Punch cewa Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha yayi kaca-kaca da Inyamuran Kasar nan inda yace ko ka kadan ba su da hadin kai kuma su ke fara ba na su kunya. A 2015 Okorocha ya taba sukar Inyamuran

Na ka ke bada kai: Idan na tsaya takara Inyamurai za su mani adawa - Okorocha

Gwamna Okorocha ya soki Inyamuran Najeriya saboda rashin hadin-kai

Gwamna Rochas Okorocha na Jam’iyyar APC yayi Allah-wadai da dabi’un Inyamuran kasar nan wadanda yace ba su ganin kowa da kima cikin mayan su da shugabanni. Okorocha yace ba haka sauran mutanen kasar nan su ke ba.

Gwamnan da zai bar kujerar sa a shekara mai zuwa ya bayyana cewa Inyamurai kadai ba su isa su tsaida Shugaban kasa ba face sun hada-kai da sauran kabilun Najeriya. Okorocha yace a ko yaushe mutanen Kasar Ibo ne ke ba da maza.

KU KARANTA: Oshiomhole ya sake ganawa da Sanatocin APC

Rochas Okorocha wanda ya ke da burin zama Shugaban kasar Najeriya yace bata lokacin sa yake yi idan har ya tsaya tunani cewa Inyamurai za su mara masa baya ya zama Shugaban kasa. A cewar sa Inyamurai ke yi wa juna bakin-ciki.

Okorocha yace ba yau Inyamurai su ka fara wannan hali na-bakin-ciki da kai-juna-kasa ba. Gwamnan yace Inyamuri sai su ajiye na su, su na hagen na waje. Hakan dai yana jawowa Yankin na Kudancin Najeriya cikas ba karama ba inji sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel