Saraki da Ekweremadu basu karfi kamu ko dauri ba - APC

Saraki da Ekweremadu basu karfi kamu ko dauri ba - APC

Jam'iyyar APC mai mulki tayi watsi da zargin da jam'iyyar PDP ke yi mata na cewar tana shirin yin amfani da jami'an tsaro domin a kama shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

PDP tayi zargin cewar APC na son amfani da ikon gwamnati domin kassara jam'iyyar adawa.

Sai dai APC din ta bayyana cewar duk da babu tushe a zargin da PDP ke yi mata, Saraki da Ekweremadu basu fi karfin kamu ko dauri ba muddin suka sabawa dokar kasa ko kuma aka same su da laifi.

Saraki da Ekweremadu basu karfi kamu ko dauri ba - APC

Saraki da Ekweremadu basu karfi kamu ko dauri ba - APC

DUBA WANNAN: Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

"Kamar yadda ta saba kirkirar karya da yada farfaganda, PDP na yada labarin cewar APC na shirin kama Saraki da Ekweremadu," a cewar Yekini Nabena, mai rikon kwaryar mukamin sakataren yada labarai na Jam'iyyar APC ta kasa.

Nabena ya kara da cewar, "gwamnatin shugaba Buhari ta tabbatar wa da duniya cewar ita mai biyayya ce ga doka da kundin tsarin mulkin kasa, a saboda haka zargin cewar za a kamu wasu mutane saboda suna jam'iyyar adawa ba gaskiya bane. Abinda ya kamata a tambaya a nan shine, me yasa 'yan jam'iyyar PDP kullum suke cikin firgicin za a kama su idan sun san basa aikata wasu laifuka?."

"Yan kasa nagari basa tsoron za a kama su saboda sun san basu aikata laifin komai ba. Amma duk wanda ya saba doka komai girma da mukamin sa, doka zata yi aiki a kansa. Gwamnatin APC ba zata ji shayin gurfanar da duk wanda ta samu da laifi gaban kotu ba," a cewar Nabena.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel