Wasu tsofaffi ma'aurata sun tsere daga gidan kula da gajiyayyu zuwa wurin Chasu

Wasu tsofaffi ma'aurata sun tsere daga gidan kula da gajiyayyu zuwa wurin Chasu

Wasu tsofaffi a kasar Jamu sun tsere daga gidan da ake kula da gajiyayyu, inda suka gudu wurin taron kida da rawa na Open Air

Wasu tsofaffi ma'aurata sun tsere daga gidan kula da gajiyayyu zuwa wurin Chasu

Wasu tsofaffi ma'aurata sun tsere daga gidan kula da gajiyayyu zuwa wurin Chasu

Wasu tsofaffi a kasar Jamu sun tsere daga gidan da ake kula da gajiyayyu, inda suka gudu wurin taron kida da rawa na Open Air, wanda wannan taro yana daya daga cikin manyan wasannin chasu na kasar Turai.

DUBA WANNAN: Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Gidan rediyon NDR dake kasar Jamus shine ya sanar da hakan, inda ya kara da cewa hukumar 'yan sandan kasar sun gano tsofaffin ma'auratan sun gudu daga gidan da ake kula da su din, sai suka dinga bin bayan su har zuwa wajen rawar, inda suka same su cikin nishadi da jin dadi.

Rahotannin sun nuna cewa akwai shahararrun mawaka irin su Judas Priest, Red Hot Chill Peppers da In Flame duk a wurin chasun, inda dalilin haka yasa tsofaffin suka ki komawa gidan gajiyayyun.

Dole yasa 'yan sandan juyawa da motar da suka taho da ita daga gidan gajiyayyun domin daukar su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel