Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Likitoci dake cikin babban birnin tarayya sun gama shiri tsaf domin tafiya yajin aiki a ranar 25 ga wannan watan, idan har hukumar lafiya bata mai da musu albashin su yanda yake ba

Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja

Likitoci dake cikin babban birnin tarayya sun gama shiri tsaf domin tafiya yajin aiki a ranar 25 ga wannan watan, idan har hukumar lafiya bata mai da musu albashin su yanda yake ba.

A wata takarda wacce shugaban kungiyar likitocin birnin Abujan ya sanya hannu a kai, yace har yanzu akwai wasu daga cikin su wadanda sun samu nasarar cin jarrabawa da ake yi ta karin girma a shekarar 2016, amma har yanzu ba a kara musu girma ba.

DUBA WANNAN: Kotu ta tisa keyar sa gidan kaso, saboda ya yiwa wata yarinya fyade

Bayan haka kuma akwai sauran kudaden ariyas da ba a biya su ba, bayan kuma an fada musu cewar an saka kudaden a cikin kasafin da aka fitar. Ya kara da cewar suna da masaniya cewar an biya wasu ma'aikatan lafiya kudaden.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel