Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin kasar ta soke dawowarta a ranar Talata

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin kasar ta soke dawowarta a ranar Talata

Majalisar dokokin kasar ba zata sawo zama a gobe Talata, 14 ga watan Agusta ba sabanin yadda Jama’a suka samu labara, jaridar The Punch ta ruwaito.

A majalisar wakilai, kakakin ta, Mista Abdulrazak Namadas ya fadaa majiyarmu cewa maganar gaskiya majalisa bata sanya rana dawowa ba tukuna.

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin kasar ta soke dawowarta a ranar Talata

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin kasar ta soke dawowarta a ranar Talata

Abun mamaki, mataimakin kakakin majalisa,Mista Yussuf Lasu ne ya bayyana a makon da ya gabata cewa majalisar dokokin kasar zata dawo zama a ranar Talata domi duba ga kasafin kudin zaben 2019 da sauran lamura da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar gayan majalisa a watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Za mu kai mamaya maJalisar dokokin kasar idan Saraki yaki yin murabus – Kungiyar yakin neman zaben Buhari

A wani lamari na daban, A ranar Litinin, 13 ga watan Agusta fadar shugaban kasa tace mukaddashin shugabna kas, Yemi Osinbajo shine dai zai kara zama abokin takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a shafukan umunta da kafofin watsa labarai, Garbe Shehu ne ya bayyana akan a wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel