Yanzu Yanzu: Buhari zai sake takara ne tare da Osinbajo a 2019 – Fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari zai sake takara ne tare da Osinbajo a 2019 – Fadar shugaban kasa

A ranar Litinin, 13 ga watan Agusta fadar shugaban kasa tace mukaddashin shugabna kas, Yemi Osinbajo shine dai zai kara zama abokin takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a shafukan umunta da kafofin watsa labarai, Garbe Shehu ne ya bayyana akan a wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.

Yanzu Yanzu: Buhari zai sake takara ne tare da Osinbajo a 2019 – Fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari zai sake takara ne tare da Osinbajo a 2019 – Fadar shugaban kasa

Kakakin shugaban kasar yace nasarorin da jam’iyyar All Progressives Congressives Party mai mulki ta samu a zaben yan majalisa da aka udanar a jihohi uku a karshen mako alamu ne na cewa babu shamaki wajen nasarar Buhari/Osinbajoa zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Abubakar ya bayyana cewa da wuya idan gwamnan jihar Kano, Abdulahi Ganduje zai zake lashe zabe a 2019.

Tsohon mataimakin gwamnan wanda yayi murabus daga matsayinsa kuma ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin cewa ya bar matsayinsa ne saboda banbacin ra’ayi da aka kasa sasantawaa tsakaninsa da gwamnan jihar Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel