Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

A jiya, Lahadi, ne kwamandan soji na ofireshon Lafiya Dole dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno ya fuskanci tirjiya da bore daga rundunar sojoji dake karkashinsa a filin tashi da saukar jirage dake Maiduguri.

Sojojin sun yi boren ne yayin da kwamandan ya bayar da umarnin yin canjin wurin aiki ga wasu dakarun sojin dake aiki a filin tashi da saukar jiragen.

Hukumar soji ta bayyana cewar yin canje-canje ya zama dole ne domin inganta aiyukan sojin a yakin da suke yi da ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram. Saidai wasu daga cikin sojojin da basu fahimci ma’anar yin canjin ba sun yiwa kwamandan tawaye tare da yin harbi cikin iska domin nuna kin amincewar su da umarnin canja masu wurin aiki.

Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

Boren sojoji ga shugabanninsu: Al’amura sun koma daidai a filin tashi da saukar jirage na Maiduguri

A wata sanarwa da hukumar ta soji ta fitar mai dauke das a hannun Kanal Onyema Nwachukwu, mataimakin darektan hulda da jama’a na rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole, ta bayyana cewar yanzu haka al’amura sun koma daidai bayan hatsaniyar da ta faru a jiyan.

DUBA WANNAN: Sanatan arewa ya gamu da fushin matasan mazabar sa saboda ya koma PDP, hoto

Kwamandan sojin, Janar Abba Dikko, ya dauki matakan da suka dace tare da daukan matakan ganin hakan bat a sake faruwa ba a nan gaba.

Hukumar soji ta bukaci mazauna garin Maiduguri da su koma bakin harkokinsu tare da bukatar su sanar da hukuma duk al'amuran wasu mutane da basu amince da shi ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel