Da duminsa: Kotun daukaka kara ta dakatar da umarnin kotu na kama shugaban INEC

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta dakatar da umarnin kotu na kama shugaban INEC

Wata kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta dakatar da umarnin da mai shari’a Jastis Stephen Pam, na wata babbar kotu ya bayar na kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Wani kwamitin alkalai 3 da Jastis Abdul Aboki ke jagoranta ne ya dakatar da umarnin kotun ta farko a yau, Litinin, bayan sauraren daukaka karar da Farfesa Yakubu ya yi, in da yake kalubalantar hukuncin mai shari’a Jastis Pam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel