Kotu ta tisa keyar sa gidan kaso, saboda ya yiwa wata yarinya fyade

Kotu ta tisa keyar sa gidan kaso, saboda ya yiwa wata yarinya fyade

A ranar Litinin dinnan ne alkalin wata kotun majistire dake jihar Sokoto, ya tura wani mutumi mai suna Kasimu Umar gidan kaso

Kotu ta tisa keyar sa gidan kaso, saboda ya yiwa wata yarinya fyade

Kotu ta tisa keyar sa gidan kaso, saboda ya yiwa wata yarinya fyade

A ranar Litinin dinnan ne alkalin wata kotun majistire dake jihar Sokoto, ya tura wani mutumi mai suna Kasimu Umar gidan kaso, saboda kama shi da aka yi da laifin yiwa yarinya 'yar shekara 13 fyade. Umar wanda yake zaune a unguwar Ubandoma dake cikin garin Sokoto, ya fuskantar hukuncin fyade.

DUBA WANNAN: Sun saci kayan dubu 50, an bayar da belin su akan dubu 400

Alkalin kotun majistiren, Abubakar Adamu, ya daure wanda ake zargin sannan ya bukaci a turo laifin nashi zuwa wurin daraktan gabatar da manyan laifuka na jiha, domin neman shawara. A karshe alkalin kotun ya dage karar mutumin zuwa ranar 30 ga wannan watan.

Dan sandan da ya gabatar da mai laifin, Umar Rabiu, ya bayyana wa kotu cewar, Kasimu ya aikata laifin nashi ne a ranar 1 ga watan Yulin shekarar nan, a cikin gidan sa. Rabi'u yace wanda ake tuhumar ya jawo hankalin yarinyar zuwa cikin dakin shi inda ya kwanta da ita.

Ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Rukayya Usman ta kai karar mutumin ne zuwa ofishin 'yan Hisbah na jihar, domin a bi mata hakkin 'yar ta.

Laifin ya sabawa sashi na 283 na dokar kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel