Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya samu matsala da matarsa Melania Trump, dalilin shahararren dan wasan kwallon kwandon nan na kasar ta Amurka wato Lebron James

Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya samu matsala da matarsa Melania Trump, dalilin shahararren dan wasan kwallon kwandon nan na kasar ta Amurka wato Lebron James.

Uwargidan shugaban kasar ta Amurka Melania Trump ta yabi dan wasan kwallon kwandon jim kadan bayan mijinta ya zazzage shi a shafinsa na sada zumunta na Twitter.

DUBA WANNAN: Barayi sun sace Kambun Sarautar wata kasa

A wata hira da Lebron James yayi da kafar yada labarai na CNN, ya bayyana cewa, shugaba Donald Trump yana raba kan mutanen Amurka, kuma yanayin siyasar wariya.

Bai jima da yin nashi jawabin ba, sai shima shugaba Donald Trump ya fitar da nashi sakon ta shafin sa na Twitter inda yake cewa, ai mutumin da yayi wannan magana a kafar yada labarai ta CNN banza ne kuma shashasha ne.

Yace a nuna James a matsayin mutum mai tunani, hakan ba abu ne mai kyau ba.

Jim kadan bayan wannan maganganu na Trump sai ita ma matarsa Melania ta bakin kakakinta ta nuna yabo ga James akan wani aikin gina makaranta da yake yi a garin Ohio dake kasar ta Amurka.

Kakakin ya bayyana cewa nan da wani lokaci kankani Melania zata iya kai ziyara makarantar domin gani da ido.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel