Kuma dai, masu zanga-zanga sun kunyata Kwankwaso sunyi masa ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgi (bidiyo)

Kuma dai, masu zanga-zanga sun kunyata Kwankwaso sunyi masa ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgi (bidiyo)

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin lemar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sake shan ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe International Airport Abuja.

Kwankwaso, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar Progressives Congress (APC) zuwa PDP ya sha kunya lokacin da ya shiga jama’a inda suke ta ihun "Sai Baba, sai Buhari", a wani bidiyo da yayi fice a shafin Facebook.

Ihun ‘Sai Buhari’ na nufin ba’a yi na’am da sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP ba kamar yadda kowa yasan taken (Sai Baba, Sai Buhari) na nufin goyon baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin bidiyon an gano Kwankwaso na tafiya cikin hadimansa.

KU KARANTA KUMA: An kama wani Mahauci da ya kware wurin yanka Kare yana gasawa ya sayarma da mutane

Wasu mutane na ta ihun sai Baba yayinda Kwankwaso ke sanye da farin kaya da jan dararsa, inda ya basar da su ba tare da ya tanka masu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel