Barayi sun sace Kambun Sarautar wata kasa

Barayi sun sace Kambun Sarautar wata kasa

A kasar Swidin barayi sun sace kambun sarautar Sarkin Karl na 9 tare da kambun matarsa Kristina, wadanda suka rayu a karni na 17

Barayi sun sace Kambun Sarautar wata kasa

Barayi sun sace Kambun Sarautar wata kasa

A kasar Swidin barayi sun sace kambun sarautar Sarkin Karl na 9 tare da kambun matarsa Kristina, wadanda suka rayu a karni na 17.

Kakakin rundunar 'yan sandan Ostergotland, Thomas Agnevik yace barayin sun sace kambunan sarautar ne a cocin Strangas dake gabar kogi wanda ke da nisan kilomita 100 daga garin Stolkhom babban birnin kasar.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen shugabannin Najeriya da kasafin kudaden da suka fitar daga shekarar 1999 zuwa yau

Ya ce, barayin sun sace kayan ne wadanda aka samar dasu a shekarar 1611 a lokacin da suka kai ziyara cocin, kuma barayin sun arce da kambunan ta hanyar amfani da jirgin ruwa.

A halin yanzu dai jami'an tsaro sun bazu suna ta neman barayin, amma har zuwa yanzu babu amo babu labari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel