Da yiwuwan majalisa ba zata dawo gobe ba kamar yadda ake zato

Da yiwuwan majalisa ba zata dawo gobe ba kamar yadda ake zato

Ana hasashen cewa majalisar dokokin Najeriya ba zata dawo zama da hutu gobe Talata ba kamar yadda ake tsammani.

Wata majiya na kusa da shugabancin majalisar ta bayyana cewa har yanzu ba’a yanke shawara kan dawowar yan majalisan ba.

Mataimakin kakakin majalisar, Yusuf Lasun, ya bayyanawa manema labarai a makon da ya gabata cewa majalisar dokokin tarayyar za ta dawo gobe Talata domin tattauna wasu al’amura masu muhimmanci.

Lasun ya bayyana cewa shugabannin majalisan sun yanke shawaran sako zantawa bayan ganawarsu da shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu, kan tabbatar da kasafin kudin hukumar domin shirin zaben 2019.

Da yiwuwan majalisa ba zata dawo gobe ba kamar yadda ake zato

Da yiwuwan majalisa ba zata dawo gobe ba kamar yadda ake zato

Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika domin bukatan kudi N242 billion na gudanar da zaben 2019.

Majalisar dokokin sun gaza mika wannan bukata kafin tafiyarsu hutu a ranan 24 ga watan Yuli, 2019.

KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

A ranan 7 ga watan Agusta, 2018, shugabannin sun shirya ganawa amma hakan bai yiwu ba bayan wasu jami’an hukumar DSS suka hana yan majalisan shiga harabar majalisa.

Majiyar ta jaddada cewa “Rikici da tuhumce-tuhumcen da ke faruwa yanzu kan zama cikas ga dawowan majalisar dattawa ranan Talata.”

Ya kara da cewa fadar shugaban kasa bata shirya sulhu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel