Sanata Shehu Sani yayi wa Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo raddi bayan ya soki Malaman addini

Sanata Shehu Sani yayi wa Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo raddi bayan ya soki Malaman addini

- Sanata Shehu Sani bai yarda da wata magana da Yemi Osinbajo yayi ba

- Mataimakin Shugaban kasar yace ba a wa’azi game da satar dukiyar jama’a

- ‘Dan Majalisar yace ana wa’azi a kai-a kai sai dai ba a aiki da shi a Kasar

Sanata Shehu Sani yace ba gaskiya bane ace Malaman addini ba su wa’azi game da satar kudin al’umma a wajen dakunan ibada. Haka dai Farafesa Yemi Osinbajo ya nuna a wani bayani da yayi.

Sanatan ya nuna cewa yana da ja kan maganaganun da Mataimakin Shugaban Kasa yayi kwanan nan inda ya zargi Malaman addini da rashin yin wa’azi da fadakarwa yadda ya dace game da sha’anin satar dukiyar Jama’a.

Shehu Sani ya goyi bayan Malaman kasar nan inda ya dace ba wa’azi bane ba ayi a Najeriya sai dai rashin daukan wa’azin. Sanatan yayi wannan bayani ne a jiya Lahadi a shafin sa na Tuwita yana mai raddi ga Yemi Osinbajo.

KU KARANTA:

A ganin ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya, laifin ‘Yan Najeriya ne da ba su amfani da karatun da ake yi masu a wajen ibada. Wannan akasin abin da Mataimain Shugaban kasa Osinbajo ya fada kenan kwanan nan.

Idan ba ku manta ba, a wajen wani babban taro na Kiristocin Kasar nan da aka yi a Jihar Enugu, Osinbajo ya zargi Malaman addini da cewa ba su yin abin da ya dace na marawa kudirin Gwamnatin nan na yaki da barna baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel